Mataimakiyar shugabar mata Ƴan kwankwasiyya mazauna Saudiyya Waheeba Sa'ad Ibrahim da aka fi sani da Waheeba Makkah ta ce Jarumin Kannywood Ali Artwork Maɗagwal butulci ya yiwa Kwankwaso.
Waheeba wadda take martani kan hirar Maɗagwal ɗin da Freedom Radio da a ciki ya bayyana cewa tsahon lokacin da ya ɗauka yana yiwa Kwankwaso bauta ₦250,000 kacal ce ta taɓa shiga tsakaninsu.
Sai dai Waheeban ta zarge shi da zama Kaza ci ki goge baki, kamar yadda zaku gani a wannan tattaunawar.
Ta ce, lokacin da suka yi yunƙurin kai Maɗagwal Saudiyya da aka ce ya kai Passport sai ya kai ƙananan hotuna maimakon Katin tafiye-tafiye, ƙarshe da kuɗinta ta biya aka yi masa.
Play wow

0 Comments