YANDA AKE CANJA SUNA KO LAMBAR WAYA A FACEBOOK
Assalamu alaikum warahamatullah jama'a ina muku fatan alheri ya kuke ya hakurin kasancewa damu a koda yaushe.
Ayau darasinmu zayyi mana bayani ne yanda zaka iya canja sunanka da kake amfani dashi ko lambar wayarka ko kuma email a facebook ko kuma password saboda haka darasin yana da mahimmancin gaske ka tsaya ka karanta daga farko zuwa ƙarshe.
Abinda zakayi shine kaje ka bude facebook ɗin naka daga nan a sama zaka wasu layi-layi guda uku daga gefen hannunka na dama sai ka dannasu kamar haka
Daga nan idan ka dannasu zasu buɗe maka ya zama tamkar wannan daga nan sai ka shiga cikin setting
Idan ka shiga cikin setting sai duba zaka ga personal information
Idan ka shiga cikin personal information zai nuna maka sunanka da lambar wayarka da email sai ka zaɓi wanda kake so ka canja sai danna kana edit
Yawwa,Masha Allah Wannan shine ƙarshen wannan darasin namu na yau






0 Comments