YAU DAI BARI A YITA TA KARE AKAN Pi Network!
Akwai wata magana da sanannen malamin philosophy dinnan na duniya dan kasar germany FRIEDRICH NIETZSCHE, wanda ya mutu shekara dari da ta wuce yake fada:-
“Sometimes people don't want to hear the truth because they don't want their illusions destroyed”
Ma’ana
“ Sau da yawa mutane ba sa son jin gaskiya saboda basa son rugujewar wani kawa zucin su”
Game da al’amarin Pi Network abu ne mai matuqar Saukin fahimta, amma kawa zucin masu mining din sa da kuma Abinda zan kira rashin fahimtar menene internet marketing, blockchain, cryptocurrency, liquidity, shiya sanya duk yadda ka kai ga fahimtar dasu bazasu fahimce ka ba.
Yanzu misali idan ka samu duk wani web developer da Internet market, kayi masa bayanin yadda Pi Network yake da users sama da miliyan talatin da kullum suke akanshi, kafin ka karasa masa labarin zai ce maka Chabdijan lallai masu kamfanin Pi Network suna samun kudin da bazai gaza Dollar miliyan daya ba a kullum.
Hujjarsa kuma itace, na farko kafin aje ko ina ya fahimci internet fiye da yadda ni da kai muka fahimce ta, sannan ya fahimci menene google form wanda yake kan Pi Network kuma yake kan kusan duk wani application har da binance,
hakanan ya fahimci yadda system na internet yake ta yadda idan kana da users da yawa kake making kudade na hauka a kullum.
Hakan ne zai sa yayi tunanin koda ace Pi zai zama gaske to fah sai sun gama neman kudin su da kai.
Shiyasa ba mamaki KYC din da akeyi suk ki bari kowa yayi lokaci daya, dan idan akayi haka za’a daina amfani da tsohon app din su.
Zai Kalli meyasa Pi bazasu bari ayi kyc kamar yadda ake na Kowane app ba, idan sunce dan tsaro ne ai basu fi binance tsaro ba, idan kuma yawa ne akwai hanyoyin zasu bi.
Wanda ya fahimci menene blockchain kuma zai kawo nashi uzurin na cewar ai kwata-kwata pi bai yi kama da asalin abinda ake kira mining na (PoW) ba a blockchain, toh amma k asancewar wanda yayi KYC suna bashi Pi kyauta wanda bawai
asalin naka bane fa da kayi mining akan ainahin app na pi ba,
kawai idan kayi kyc ne suka tabbatar da ingancin kyc din naka,
sai su samu wani portion na transferable balance dinka su ba.
Ba mamaki karya Nicolas yayi na cewar mining akeyi a Pi Network, maybe ba mining ake ba. Dalili shine idan mutum yayi staking kamar yadda suka fada a cewar su (Lock up) zasu dinga baka wani percentage, kaga kenan yanzu blockchain din da ake mining (PoW) ya dawo (PoS).
Kai bazaka fahimci wannan chakwakiyar rainin wayon ba amma Cikakken blockchain developer yasan me ake nufi anan.
Sabasa haka Idare not you, a typical pi network miner but i mean Nicholas himself ya fito yayi bayani.
Abun kuma idan muka dawo muka masa kallon cryptocurrency wata sabuwar chakwakiyar ce .
Munsan dai duk wani cryptocurrency yana buqatur zunzurutun kudin liquidity kafin a iya mu’amalar kasuwanci dashi koh? Toh Pi dai yana da Total supply billion dari, kuma babu wani tokenomic da yake dashi wannan 100 billion din du raba shi za’ayi ga mutane, kuma sai an gama mining sannan suka ce zasuyi launching.
Kaga kenan kafin Pi Network ya fito a iya hada-hada dashi a farashin da mutane suke fada, toh yana buqatar liquidity na malala gashin tinkiya a taikaice. Toh amma sunce ai Pi network ba cryptocurrency bane, shi kudi ne na kan shi da kan shi.
Za’a masa creating ecosystem nashi na kansa ba ecosystem na crypto da normal kudin takadda ba. To a nan ne
wadanda suka fahimci menene liquidity sukayi kaca-kaca da Nicholas.
Tunda nan fanni na ne bari nayi fashin bakin da kaina .
Abokina liquidity yana nufin wani ma’auni da ake gwada saurin yadda kowane kalar abu da ka sani a duniya ake iya saurin chanza shi zuwa normal kudi.
Yanzu misali. Fili a cikin garin abuja yafi a cikin kauyen ku tsada, sannan sai anfi saurin siyar da fili a cikin abuja fiye da a cikin kauyen ku.
Hakanan yanzu wayar smartphone ta Apple tafi tsada idan zaka siye ta a matsayin sakan fiye da android, toh hakan still na nufin apple sunfi android daraja wanda daidai yake da Liquidity a kasuwa.
Zaka iya zuwa kasuwa ka samu abu suna da komai iri daya amma daya yafi daya tsada.
Toh wannan ma Liquidity ne.
Wannan kadan daga cikin ma’anar liquidity a kasuwar zahiri, idan ka fahimci wannan ma’anar to kaga kenan komai a duniya yana buqatar liquidity kafin ayi kasuwancin shi.
Idan muka dawo kasuwar chanji ta kudaden duniya kuma zamu sama tsinanniyar dalar amurka tafi kowane kudin duniya daraja, ba ina nufin tsada ba, daraja nake nufin ta liquidity.
Shiyasa ba inda bazaka je ka kashe dalar amurka ba a duniya,
amma banda lalatacciyar naira ta baba buhari.
Wannan ma’auni ne dake nuna maka cewa dalar amurka tafi Naira liquidity.
Kaga sabanin a baya fassarar liquidity ta dauki daraja ta kaya, a nan kuma fassarar liquidity da dauki daraja ta adoption, ma’ana zunzurutun masu amfani sa dollar.
A takaice kuma fassarar liquidity a crypto, liquidity yana nufin saukin yadda zaka iya trading na coin a kowacce exchanger a baka dollar cikin sauki.
Wannan kuma holders ne suke kawo
wannan darajar da kuma traders.
Yawan adadin exchanger da sukayi listing din token, toh yawan liquidity din da zai dingasamu.
Fassarar na iya daukar abubuwa da yawa amma nayi muku ita a takaice.
Toh mu dawo mu kalli Pi Network da yadda za’a masa providing liquidity, yanzu dai idan kun fahimta liquidity bawai yana nufin kudi da za’a zuba a coin ba kamar yadda yan Pi
Network suka dauka.
A’a yana nufin karbuwa, kadara, inganci, yardar hukumomi da sauran su. Sannan kafin abu ya samu duk
wannan darajar sai ya zama scarce Ma’ana kadaan ne.
Shiyasa saboda zamewa duk wannan formalities din sai mai project din Pi Network nicholas yace za’a kirkirarwa Pi Network ecosystem dinsa ba irin wannan ba.
Sunce shi za’a kirkirar masa inda zakaje ka kayi amfani dashi wato Pimall.
A nan ne yan kasuwar da suka yarda zasu karbi Pi su bayar da dukiyar su zasu dinga cikayyar duk Pi daya a
farashin $314,000 wanda shine official price na Pi, to amma ta yaya? Ko a yanzu masan idan akace iya wadanda suke da Pi din su fito su yi kasuwanci shi, to ko kasuwar duniya bana tunanin zata iya proving kayan masarufin da zasu bayar su karbi Pi.
Kai a siyar da har gidanku, takalmin kafarka da da komai sa ake kasuwancin sa a duniya bai kai kayan masarufin da ake buqata ba ya wadatar sa kasuwar Pi.
Sannan bugu da kari wane dalili zai saka su yan kasuwar su karbi Pi a matsayin kudi? Dole yana buqatar abubuwan nan dana fada na liquidity kafin su yarda su karbe shi din. Sannan mafi girman problem din da ban taba ji wani yayi maganar shi akan Pi ba shine.
Daga cikin abinda kowane kudi yake buqatar kafin ya amsa sunan shi kudi toh yana buqatar scarcity, misali.
Gold yana da wahalar nema, bitcoin akwai wahalar mining, ba sai munyi maganar kudin takadda ba wannan gwamnati taqaqaba mana.
Amma shi pi network ina da guda dubu shida?
Akwai kuma irina da suke da dubbunan Pi mu miliyoyi.
Dan Allah fada mini tayaya cikakken san kasuwa mai hankali sa hangen nesa zai karbi Pi network a wannan darajar da kake magana, bayan yasan cewa akwai shi a banza a hannun
miliyoyin mutane, sannan kunce ai Pi kudine na duniya, waye
ya fada maka mutum miliyan talatin da suke mining Pi iya sune kadai a duniyar? Bari na gaya maka duk abinda ka sani kafin ya zama kudi yana buqatar liquidity dinnan da bakwa son kuji anyi maganar shi.
Magana ta domin Allah ka yarda ko kar ka yarda kamfanin Pi Network suna neman kudi dakai, sannan farashin da kake magana bazai fito a haka ba.
Hakanan launching dinsa ba nan kusa ba, sannan bugu da kari zancen Pi zai fito nan kusa da kamar wuya .
Idan Allah yasa mun samu kudi dashi tom
Alhamdulillah,
Idan kuma akasin hakane to
Allah ya isa bata mana lokaci da akayi.
Bissalam
Wallahu Ya’alamu….
Author: Muhammad Sheka
Post by msz Tech...


0 Comments