Ad Code

Responsive Advertisement

YADDA ZAKA SAKA BLUE LIGHT FILTER A WAYARKA DOMIN BAMA IDONKA KARIYA DAGA HASKEN WAYA.


 YADDA ZAKA SAKA BLUE LIGHT FILTER EYE PROTECTOR A WAYARKA DOMIN BAMA IDONKA KARIYA DAGA HASKEN WAYA.


Kada ku sha'afa wajen jin da'din ta'ammali da wayoyinku ba tare da kuna bama idonku kariya da hasken wayarku ba.


Tabbas hasken waya yana cutar da idanu mussaman ma idanun mutanen da suke amfani da wayarsu a cikin duhu, wanda zai zamana hasken wayarne kawai yake haska masu ido, domin idan ya kasance babu wani haske a inda mutun yake sai hasken wayarshi, hakan zai ƙara ma hasken wayar tashi ƙarfi, ta dalilin hakan hasken wayar zaifi samun damar haske idanun mutun baki 'dayansu.


Allah ya haliccemu kowa da irin halittar da Allah yayi mashi, wasu suna da raunin idanuwa, wasu kuma basu da wani rauni a tattare da idanuwansu, to koma kana da rauni a idanuwanka koma baka da rauni a idanuwanka, kula da lafiyar idonka wajibi ne 'dan'uwa, bare ma a irin wannan lokacin da muke ciki, babu abunda muke amfani dashi sama da wayarmu ta hannu.



Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen kula da lafiyar idanu, dan kada hasken waya yayi masu illa.


Wasu wayoyin suna zuwa da eye protection mode, zaku ganshi yana da alamar zanen ido, idan kuka jawo labulen wayarku na sama inda kuke zuwa idan zaku kunna datar wayarku.


BLUE LIGHT FILTER EYE PROTECTOR app ne wanda yake da features masu yawa, koda ace wayarka tana da eye protector mode zaka iya download na wannan app 'din domin yana da matuƙar amfani.


Danna nan domin sauke app din

                        👇

         eyefilter.nightmode.bluelight filter apk


Steps da za kubi wajen saitashi a wayarku:


1- Banyan kunyi installing 'dinshi a wayarku, kuna bu'deshi zai nuna maku (0/2 permissions) sai ku danna wajen.


2- Daga nan zai baku damar ku kunna permission na farko, sai ku kunna, ku danna back.


3- Zai dawo daku baya idan kuka danna back, amma za kuga inda ya rubuta maku (0/2 permissions) ya koma (1/2 permission) alamar kun kunna 'daya saura 'daya, sai ku ƙara danna wajen, shima zai kaiku inda zaku kunna permission na biyu.


4- Anan ma bayan kun danna back za kuga ya kawo ku wani waje da aka rubuta "Let's Go" sai ku danna wajen, kai tsaye zai kaiku inda za kubi ku ƙarashe saita app 'din.


5- Daga can sama a hannun damarku za kuga inda aka saka wani makunni mai alamar OFF, shine zaku ta6a, da zaran kun ta6ashi zai koma ON, shi kenan kun kunna app 'din, kun bashi damar ya fara aiki akan wayarku, tun anan za kuga hasken wayarku ya chanja.


6- Daga cikin features 'dinda nace maku app 'din Blue Light Filter yana dashi sune na zagaye maku su a hoton daga gidan da 6 take.



Zaku iya saita lokacin da kukeso app 'din ya fara aiki, tare da sauran wasu abubuwan da zaku gani a ciki.


Allah yasa mu dace🙏

Domin Karin 

bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za'a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 


Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

KIRA : 08135986732 

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement