YADDA AKE TSIRE TA HANYA MAFI SAUKI.
Salam Barkan mu da wannan lokaci Cikin Topic Namu Mai farin Jini Wato DABARUN GIRKE - GIRKE.
Yau Ma mun zo muka da YADDA AKE HADA TSIRE Saka Mai gida Santi Saka Saura yi Sanbatu.
*YADDA AKE TSIRE*
1-Kayan Hadi
2-Jan nama
3-Albasa
4-Yajin barkono
5-Kuli kuli (gari)
6-Kayan kamshi(garlic da citta)
7-Man gyada
8-Maggi
*YADDA ZAKI HADA*
1. Da farko zaki tanadi tsinkenki idan kina bukata ki wanke shi, idan so samu ne ki bar tsinken yin tsiren a ruwa yayi wasu mintuna ko awa 1. Yin hakan zai Hana shi yayi kamu yayin gashin.
2. Dama kin tanadi jan naman ki maras kitse sosai👌. Sai ki yanka namanki yayi fadi ba sosai ba saiki zuba acikin bowl kisa garin barkono,garin tafarnuwa, Maggi,gishiri kadan saiki juya sai ki kawo garin kulikulinki ki zuba ki juya sosai yanda ko Ina zai ji.
Saiki zuba mai ki juya sosai ki rufe sai ki barshi na dan wasu mintoci, sai ki dauko tsinke ki ki jera ajiki.
3. Zaki samu wani plate ki zuba kulikuli, Maggi, garin barkono ki juya sosai saiki dinga dauko naman kina sawa ajiki ko Ina yaji saiki jera a akan abin gashi, idan Kuma kina da oven sai ki gasa abin ki lfy.
Idan Kuma baki son yin amfani da tsinken tsire, idan duk kin gama saka kayan hadin ki a cikin naman sai ki kawo tukunya ko kasko (frying pan) mara kamu sai ki jera ki dora a wuta ki rufe ki barshi.
Note :
Kar ki sa wutar tayi yawa Sai ki ringa juyawa, idan yayi zaki ji gidan ya dauki kamshi sai ki sauke ki yanka dai dai misali kisa sa plate ki yanka albasa da kabeji da tumatir da koren tattasai ki zuba idan kina bukata.
Aci dadi lfy 😋😋
Post Bye ummu walad🖋


0 Comments