Fitattun jaruman Bollywood da suka fi biyan kudin haraji a India.
- Shah Rukh Khan
Yana cikin jaruman da suka shigo da kafar dama a masana'antar, inda tauraronsa ke cigaba da haskawa a Duniyar fina-finai. Jarumin ya biya haraji sau tari wanda ya kai akalla 5 crores.
- Amitabh Bachchan
- Salman Khan Ko Bollywood's Bhai
Jarumin yana jan zarensa a masana'antar, kuma yana cikin manyan jaruman da suke rayuwa mai tsada. Harajin da yake biya a kwanakin nan yana kan 10.5 crores.
- Akshay Kumar
Jarumin yana daya daga cikin jaruman da ke samun albashi mafi tsoka a Bollywood, sashen haraji na Income Tax, ya bayyana jarumin a matsayin wanda yafi biyan haraji mafi girma A kasar cikin shekaru biyar da suka gabata, ya biya kusan 11 crores.
- Aamir Khan
Fitaccen jarumin da ya yi suna a fim din Laal Singh Chaddha, ya biya 4 crores a matsayin haraji. Yana yin fina-finai kaɗan ne kawai a shekara, amma har yanzu yana cikin masu biyan kuɗin haraji mafi girma a Indiya.
- Superstar Rajinikhanth
Jarumin da aka fi sani da Thalaiva, a hukumance shi ya fi biyan haraji mafi yawa a Tamil Nadu. Sashen harajin kudin shiga na jihar ya karrama jarumin wanda aka gani na karshe a fim din Annaatthe na 2021, ya biya haraji kusan rupi miliyan 9.
- Hrithik Roshan
Jarumin ya kasance cikin jerin jaruman da ke biyan haraji a kaia kai, jarumin yana bayyana yadda yake rayuwa mai TSADA, amma ko yaushe yana gaggawar biyan harajinsa. Inda ya biya fiye da miliyan 4 na rupi.
- Deepika Padukone
Tana daya daga cikin jaruman Bollywood da suke samun albashi mafi tsoka, kuma ba mamaki ta kasance daya daga cikin manyan masu biyan haraji a Indiya. Ta biya harajin Kusan 3 crores.
- Ranbir Kapoor
Jarumin ya gamu da rashin nasara a shekarun baya A masana'antar, amma har yanzu yana ci gaba da kasancewa daya daga cikin masu biyan haraji. Har ma ya biya haraji Kusan 3 crores.


0 Comments