- Brise Token Fundamental Analysis
"The main idea na yin FA da nake bawai inayi ne dan mutane suje suyi investing ba, a'a ina yi ne saboda mutane su fahimci menene dalilan da suke sakawa a Kalli token har a dinga praising dinsa ana cewa ayi investing mai kyau ne.
Ni ina ga a maimakon naje Kai tsaye nace maka kaje ka siyi token kaza mai kyau ne, gwara na fada maka dalilin da Yasa ya zama maikyau din idan yaso in kana da ra'ayi sai kayi investing"
"Not A Financial Advice"
(1) What is Brise Token
Brise token ne da yake kan BEP20, ERC20 da kuma BRC20, kuma ya samu gatan team din da suke kwararru akan harkar Blockchain, kamar dai Saitama da FEG.
Shi ma brise hyper-deflanationary token ne (Ma'ana token din da suke rewarding dinka saboda hodling).
Amma sabanin Saitama da FEG da suke rewarding da token din su, shi brise suna rewarding dinka ne da BNB.
Brise shine cryptocurrency na farko da yake da tsarin zamani da Automatic BuyBack, sannan kuma sabanin sauran cryptocurrency da suke da use case na karya, shi kam brise ba haka abun yake ba.
(2) Roadmap
Daga cikin abubuwan da project suke so su cin ma a Roadmap dinsu abubuwa ne guda sha biyu, Kuma alhamdullillahi sun cika alkawarin yin guda hudu Wanda daga ciki har da KIRKIRAR Blockchain da suka alkawarta, sai kuma na biyar da suke kan yi a yanzu da suke kirkirar PayBrise DApp, sannan kuma akwai na bakwai Wanda suke son kirkirar decentralized market place kamar trust wallet da kuma centralized wallet da suke son yi.
A dai yadda suka tsara zasu ci gaba da yiwa project din aiki har zuwa 2025 nan da shekara uku kenan.
(3) About Brise Token
Anyi launching dinsa a watan august, Wanda da a lokacin ka siye shi a pancake zuwa yau to ya ninka maka kudinka sau adadin da yakai ka lissafa shi a riba.
Total Supply
yana da total supply 1 Quadrillion, ba'a san takamaiman circulating supply dinsa ba amma last week yana da total supply 456trillion,kaga kenan
kusan Rabin total supply dinsa yana hannun mutane. Sannan yana da Marketcap 389million, hakanan yana da total trading volume na 18million.
(4) Conclusion
A cikin shekarar da ta wuce ne team din brise suka yi nasarar kirkirar Blockchain nasu na kansu Wanda yake da saurin transaction daya ninka Bitcoin sau dubu ashirin, sannan ya ninka Ethereum saurin transaction sau dubu hudu, tron sau dubu biyu.
Hakanan ya ninka Visa da Master Card saurin transaction sau hamsin, idan kayi transaction ta Blockchain din brise cikin kiftawar ido zai zo.
A kullum ana transaction da Brise sau dubu saba'in hakan ne ya basa damar zama the fastest growing Blockchain project, sannan yana da community da yakai na fiye da mutum dubu dari da talatin.
Sannan Blockchain na brise (BRC20) bashi da gas fee ko daya, sai anyi transaction sau miliyan dari sannan masu project din zasu samu value na transaction daya kai 1$.
Brise DeFi project ne da masu kamfanin suke son nan gaba su dora tsarin NFTs da kuma Web 3.0.
Idan kana son kara fahimtar abun da muka tattauna zakayi iya zuwa Kai tsaye ka saurara a telegram group din mu.
Post by
Muhammad Abdulrahman Sheka.


0 Comments