Ad Code

Responsive Advertisement

YANDA AKE HADA KILISHI TA HANYA MAFI SAUKI.


YANDA AKE HADA KILISHI TA HANYA MAFI SAUKI. 


Salam Barkan mu da wannan lokaci Cikin Topic Namu Mai farin Jini Wato DABARUN GIRKE - GIRKE. 

   Yau Ma mun zo muka da yadda zaka ko Zaki hada KILISHI Saka Mai gida Santi Saka Saura yi Sanbatu. 


                *YANDA AKE KILISHI*        


Kayayyakin Hadi Sun hada kamar haka :-


➡️Nama( Mara kitse dayawa)


➡️Kulikuli


➡️Maggi


➡️Albasa


➡️ other spices


        

               *YADDA ZAKI HADA*         


 Da farko idan kin wanke namanki kiyanka shi fale fale se kisa a inda ze bushe sosai don Yana bukatar Rana sosai don idan Babu Rana ma yakan dauki kwanaki bai bushe ba.


 Idan ya bushe seki hada garin kulikulinki dasu maggi, spices dinki zaki iya sa barkono idan kinaso sai ki kwaba da ruwa yayi ruwa ruwa seki dauko busheshshen namanki ki shashshafa hadin kuli kulin ajiki ko Ina yaji sosai zaki kara shanyan shi kafin ki gasa. Zaki iya amfani da oven ko waya wajen gasawa.


Za kuma ki iya idan kin yanka namanki sai ki jera a tray kisa a oven ya danyi sai ki dauko kishashshafa hadin kuli kulinki sai ki mayar oven din yakara gasuwa.


Kilishi ya kammalu 👌

Aci dadi lfy 😋

Presented bye ummu walad🖋


Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement