SHIN DOGE ZAI IYA TABA $1 KAFIN KARSHEN 2022 KAMAR YANDA AKAYI Hasashe.
A yayin da farashin doge me cigaba da tabuwa kamar dai sauran coins masu trading da holding na mamakin cewar Shin ko zai Kai matsayin da akayi ta hasashe a baya kuwa na kaiwa $1?
Kamar yanda bayanai suka nuna daga shafin COIN MARKET CAP a yau 26 ga July ana trading din Doge akan $0.06104
Hakan na nufin yana nesa da $1 da kashi 93.869%.
Hakazalika ta FUSKANCIN market cap din sa ya rasa Karin Kashi 5.9% ya sake rasa 9.80 duk acikin makwanni biyu da suka GATABA.
Abinda ya sa market cap dinsa ya dawo $8.11B daga $85 billion daya taba kaiwa a ranar 5 ga watan Mayu na 2021 lokacin ELON yana KURURUTA shi.
Duba da yadda kasuwar CRYPTO take kwangaba kwan baya Da Kuma yadda market cap na doge din ya kusan RUSHE gabaki daya.
Wasu MASANA na ganin cewar babu batun $1 nan kusa ga Dogecoin.
Written by | Gonar Bitcoin And msz hausa.
Gargadi na haɗari : Kasuwancin Cryptocurrency yana ƙarƙashin haɗarin kasuwa mai girma.
Da fatan za kuyi kasuwancin ku bi A hankali. Ana ba ku shawarar cewa MSZ HAUSA ba shi da alhakin asarar kasuwancin ku.


0 Comments