SUNNONIN RANAR EIDI
1. Yin Wanka
2. Saka Sababbin Kaya Ko Masu Kyau
3. Sanya Turare
4. Cin Dabino Kafin A Fita Zuwa Masallaci
5. Fitarda Zakkar Fidda-Kai Kafin A Tafi Eidi
6. Yin Kabarbari Har Izuwa Lokacin Da Limami Yazo
7. Yin Sallah Acikin Jam'i
8. Canza Hanyar Dawowa Gida Daga Eidi
Waɗannan Wasu Ne Daga Cikin Sunnonin Ranar Eidin Ƙaramar Sallah Wanda Idan Baka Aikatasu Ba Edinka Bai Lalace Insha Allahu, Amma Saidai Kabar Falala Mai Tarin Yawa.
NASIHAR BARKA DA SALLAH
"Babu Laifi A Ranar Sallah Za'a Iya Yin Wasa Wanda Bai Saɓawa Shari'a Ba, Da Duk Wasu Nau'ukan Al'adun Da Basu Ci Karo Da Addinin Musulunci Ba Ga Maza Ko Mata, Matuƙar Hakan Bazai Kaiga Saɓawa Allah Ba"
-
"Ya Zama Wajibi Mata Su Guji Yin Mummunar Shiga Wacce
Zata Bayyanar Da Tsaraicinsu, Su Guji Yin Shigar Banza Wai Da Sunan Murnar Sallah, Yin Hakan Ka Iya Jawo Fushin Allah, Kuma Hakan Na Iya Jawo Lalacewar Aiyukan Alkhairan Da Aka Gabatar Acikin Watan Ramadana Da Ya Gabata"
-
"Kada Mu Bari Hidindimun Bukukuwan Sallah Su Shagaltar Damu Daga Ambaton Allah Maɗaukakin Sarki, Da Kuma Yin Ibadu Na Yau Da Kullum Akan Lokaci"
ﺍﻟﻨﺼﻴﺤﺔ ﺍﻟﻌﻴﺪ
Written By Amana Islamic Medicine


0 Comments