Shawarar da zan bawa Yan uwa shine kada kaga ana dip ka dauka irin dip din daka saba ganine l! ba irinsa bane domin wannan dip din kwan gaba kwan Baya ne Yana tare da mayhem, Pandemonium, masu sayen dip dinma a tsorace suke sbd breaking na manya manyan support Idan yazama dole sai kasayi dip ka tabbata kudin baka da matsala dasu sannan kasaka stoploss A crypto komai Mai yiwuwane.
BTC.....
"Abinda yake faruwa na kasuwar crypto na mugun dip dinnan a yanzu juyin juya hali ne da ake samu na cigaba.
Abokina dominant na BTC ake so a rage, saboda matuqar ba'a rage shi ba kasuwar crypto bazata taba kaiwa inda ni da kai muke tunanin zata kai ba. Ba ina nufin kudinsa za'a rage ba ya zamana cewa darajar sa ta karye ba. A'a koda ace BTC zai kai 100k wannan shekarar toh ba'a so ya samu karfin da har zai iya kaiwa 41% da yake a yanzu ba.
Su Elon, CZ da sauran manyan yan crypto na duniya sun san me suke. Ba yadda za'a yi su saka kudi cikin kasuwar da abu daya ke da 41% na total MarketCap din kasuwar.
Jira ka gani abokina zai wahala BTC ya sake samun irin wannan damar da yake da ita a baya har abada. Abokina ko kasan cewa dominant din da BTC yake dashi a kasuwar cryptocurrencies yana daya daga cikin Dalilan da suka hana crypto karbuwa a mafiyanwancin kasashen duniya, saboda babu yadda za'a yi sovereign state ta yadda ake faduwar wani kudi zai shafi kudin kasarta.
Idan kuma mu nigeria mun yarda, toh su kuma kasashen da suka san ciwon kansu irin su china, america, russia, england, Germany, France E.t.c bazasu yarda ba."
Nasha fadawa mutane babu wani dalili na kai tsaye daya tabbatar da cewa lallai idan BTC ya fadi dole sai sauran tokens sun badi.
Abinda nake nufi dalili na kai tsaye shine ace duk faduwar BTC to akwai wani kaso na Altcoin da suke biyan sa
na faduwar. Abokina kaje ka duba duk dalilin da za'a baka faduwar Altcoin idan BTC ya fadi kame-kame ne, kowa da dalilin da zai baka.
Cikin dalilan abu mafi karfi shine za'a ce maka shine yake da kaso kuma hamsin na jarin kasuwar, kuma shima wannan dalilin theory ne kawai.
Mentality ne da aka dora mana kuma yake amfani. Ka kula ka lura sosai meyasa token din da ake kirkira yanzu zaka ga suna ta tashi ba ruwansu da wani BTC.
Idan shine yake sawa kasuwa ta tashi ko ta sauka ya hana su mana?
Meyasa tsofaffin tokens ne na baya sosai suke fadawa cikin masifar BTC?
Akwai tambayoyi da yawa daya kamata ka dinga wa kanka.
Abokina bakomai ake gani a chart analysis ba ko kuma whitepaper, wani lokacin sai ka bibiyi abinda yake faruwa a zahirin gaskiyar duniya.
Wani mentality ne aka dora mana na idan kaga BTC yana sauka toh kayi sauri ka debe kudinka daga kasuwar, idan kuma ya nuna zai tasi to kayi sauri ka shi, shine kawai. Abinda yake
faruwa idan BTC ya tashi whales suka ci riba toh zasu yi tacirar kudin suna sawa a altcoin da suke bear market. toh da zarar munga alt dinnan sun nuna alamar tashi mu kuma masu
dala goma zamu zo muyi ta FOMO shikenan sai kuma su kara cin riba su whales daga nan zasu.
A haka kasuwar take circulating a baya kenan, to amma yanzu challenging din wannan zaluncin kasuwar take neman yi.
Wannan shine juyin juya halin da ke shirin faruwa.
Shiyasa BTC yaki kaiwa inda suke so yakai saboda suna tsoron
market dominace dinsa zaiyi yawa sosai wanda hakan zai dakushe musu wata dama kuma da suke son samu a kasuwar.
Shiyasa aketa yawo damu. Idan kayi hakuri kayi surviving din wannan revolution din na duniyar crypto to zakaji dai nan gaba.
Dole za'a damu mafita, kuma ka rubuta ka aje zuwa karshen shekarar nan da shekara mai zuwa kasashen duniya dayawa zasu fara karbar crypto hannu biyu.
Toh sanin zasu karbi harkar shiyasa wasu tsirarun mutane suke son samun karbi a kasuwar, saboda sun san yanzu fa karfin kasuwar crypto yana gurin BTC.
Wadannan mutanen manya na crypto suna son kirkirar wani yantaccen tattatalin arziki da kowa yake da dama a ciki a yadda suke fada kenan.
Amma cikin zuciyar su, suna son su
kirkirar wa kansu wata dama da zasu iya juya duk wata gwamnati ne ta duniya. Wanda bazai taba tabbata suyi hakan ba har sai sun karbi iko da kasuwar wanda yanzu take hannun
BTC. Muje zuwa, mudai yan kallo ne.
Wallahu ya'alamu.....
Allah yabamu ikon jure wannan mummunar Asara.
Posts by Muhammad Abdulrahman Sheka
Reading more.... Kada Ka Sake Kayi Aure Har Sai Ka Mallaki Wadannan Abubuwan:
Reading more.... Muhawara-tsakanin-kasuwa-da-maaikacin.html Gwamnti
Reading more.... Wasu-daga-illolin-fina-finan-hausa.


0 Comments