Kamar yadda jaridar Legit.ng Hausa suka ruwaito.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa kada wani ya gayyacesa kotu amsa wasu tambayoyi kan yadda yayi mulki bayan ya bar Ofis a 2023.
Buhari yace duk wanda ya gayyacesa za suyi rikici saboda duk abinda suke bukata na rubuce a kasa Ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da gidan talabijin Channels ranar Laraba.
Yayinda yan jaridan Channels suka tambayesa shin ya nada matsala da wanda za gajesa, Buhari yace:
Yana Mai amsawa da cewa:
"A'a, ko waye yazi. Komai na rubuce. Kada wanda ya kirani kotu gabatar da wani hujja, idan ba haka ba, zamu yi rikici saboda komai na rubuce. Na tabbatar da hakan."


0 Comments