Yatsu basa taɓa zama ƊAYA Duk inda Allah ya ajiye MACE nan yake so ya ganta.
Ko kinsan wata tana nan tana murna MIJI ko IYAYE sun bata 10k na kayan Sallah,ta ɗaga Hannu ta yiwa Allah godiya kuma ta yi matuqar Farinciki har cikin zuciya?
Ko kinsan wata an bata 50k ta sayi kayan Sallah ta kasa sukuni
zuciyarta kamar za ta fashe don Qunci don bata san me zai
saya mata me mahimmanci domin Adon sallah ba saboda sunyi matuqar yi mata kaɗan? Sai kamar 100k zuwa sama haka a maleji?
•
Ko kinsan wata ko qyalle bata gani ba da sunan kayan Sallah me MIJI ko mara MIJI kuma Hankalinta kwance,tana Godiya ga Allah tana Farinciki da Addu'ar idan ba ayi wannan sallar ba za ayi a wata ko kuma wata rana za ayi mata idan Allah ya hore?
•
Ko kinsan wata MIJI ko Iyaye ba'a mata kayan Sallah duk sallah kuma ta saba da hakan? wasu babu ce, wasu kuma idan mazajensu ne Qeta ce na wasu Mazan basa yi kuma baza suyi
ba?
Ko kinsan WATA akwai da babu ita dole sai anyi mata kayan Sallah Numfashi kyakkyawa ba'a isa anyi ba idan ba'a mata ba,wata ayi tashin Hankalin ayi mata wata kuwa ta yi a wofi?
KU SAURARA!!!
Idan an samu a godewa Allah,idan ba'a samu ba ayi fatan Allah ya hore a samu a gaba, muyi Koqari idan za muyi abu muyi me yuyuwa! Ina nufin duk abin da baza mu iya sauya shi
ta Hanyar lumana ba zafi ba zai ba mu shi ba muyi Qoqari mu koyi wadatar zuci da haquri mu yaqi zuciya
Allah shi datar damu. Ameeen.
Written by
Abubakar dansarki


0 Comments