Ad Code

Responsive Advertisement

Maniyyata Najeriya sun koka a kan tsadar kuɗin aikin hajjin bana 2022.

 

Aikin Haji 2022: Maniyatta aikin hajjin bana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan sanarwar da hukumar alhazai ta kasa a Najeriya ta fitar kan kudin aikin hajjin bana. 


Duk da cewa an rika hasashen cewa kudin hajjin bana zai karu sakamakom matsin tattalin arziki da tsadar dala amma maniyyata ba su yi tunanin cewa al'amarim zai kasance haka ba.


A ranar Alhamis ne Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya wato NAHCON ta bayanna cewa za a kara kudin aikin hajji da akalla kashi 50 cikin 100 kan abin da maniyyata suka biya a 2019.



Hukumar ta yi hasashen cewa kudin aikin hajjin bana ba zai gaza naira miliyan biyu da rabi ba.

NAHCON ta alakanta ƙaruwar farashin da yanayin tattalin arziƙi da kuma hauhawar farashin dala, sai dai wasu maniyyata na cewa ya kamata gwamnati ta yi duba na tsanaki kan lamarin.

Wani maniyyaci ya shaida wa BBC cewa kusan shekara biyu ke nan da biyan kudinsa, amma karin ba zai hana shi neman hanyoyin samun ciko domin kammala biyan kudin aikin hajjin ba.

"Gwiwata ba ta yi sanyi ba. Shi abu ne na hukuncin ubangiji. Idan Allah ya yi kiran ka toh za ka amsa kiransa kuma cikin hukuncin ubangiji za mu tafi nema mu ga mai Allah zai yi mana,"in ji shi.


   

   Sai dai ya yi kira ga gwamnati a kan ta taimaka wa talakawan da ke son su je kasa mai tsarki.

"Mun ajiye kudin nan kusan shekara biyu a hannun gwamnati, toh ya kamata a ce an duba an tausaya, ta san mai za ta yi ta agazawa wannan aikin hajji da aka shafe shekara biyu ba a yi ba."

Ita kuwa wata mata waddake burin sauke farali ta gaya wa BBC cewa hankalinta ya yi matukar tashi da jin labarin karin kudin saboda kudin da ta biya a baya da kyar ta hada su.


"Gaskiya na ji kamar ba zan iya ba saboda tun lokacin da sakon ya same ni, gaba daya duk tunani na ya rikice, ina ta tunanin yaya ma zan yi na samun cikon wannan kudin."


Suma kamfanonin shirye-shiryen tafiye-tafiyen aikin hajji da Umrah duk sun sun koka da karuwar farashin kujerun aikin hajjin.


Hukumomin Saudiyya sun ware wa Najeruya kujeru fiye da dubu 40 cikin maniyyata miliyan daya da ta ce zata amince su gudanar da aikin Hajjin bana.


Kafar yada labaran kasar ta ruwaito mahukuntan kasar na cewa dole mahajjatan da za su je aikin Hajjin na bana su kasance 'yan kasa da shekara 65, kuma dole sai an yi musu rigakafin korona cikakke.


A shekarar da ta wuce 'yan kasar dubu 60 ne kadai suka yi aikin Hajjin.

A shekarun baya kafin bullar korona Musulmi daga sassan duniya kusan miliyan biyu da rabi ne ke aikin Hajjin.


Source : BBC Hausa. 

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement