Ad Code

Responsive Advertisement

Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Sami Amincewar Buƌe Bankin MoMo A Najeriya.

MTN ya samu amincewa ta ƙarshe don gudanar da bankin sabis na biyan kuɗi.

Babban Bankin Najeriya ya baiwa Momo Payment Service Bank Limited izinin fara aiki. 


Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kamfanin, Uto Ukpanah, a ranar Litinin.


 Wannan na zuwa ne bayan da CBN ya amince da kamfanin ya fara aiki a watan Nuwamba 2021. 


Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya sami amincewar hukumomin Najeriya domin ya bude banki, kamar yadda kamfanin ya sanar ranar Litinin.


MTN ya ce “Babban bankin Najeriya ne zai sanar da ranar da aka amince mu fara aiki, kamar yadda doka ta samar.”


Sanarwar ta kara da cewa, “Muna mayar da martani ga sanarwar da aka bayar a ranar 5 ga Nuwamba, 2021 inda muka sanar da samun amincewar bisa ka’ida daga CBN na Momo PSB.


Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria Plc ya sanar da samun wata wasika A Cikin  8 ga Afrilu 2022 daga bankin CBN zuwa Momo PSB yana isar da izini na karshe don fara aiki.

Za a sanar da ranar da za a fara aiki ga CBN kamar yadda yake bukata.


 "MTN Nigeria ta tabbatar da kudurin sa na hada-hadar kudi na CBN da Tarayyar Najeriya kuma muna farin cikin da wannan damar da za mu goyi bayansa."

Post by msz Tech. 

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement