Ad Code

Responsive Advertisement

Elon Musk: Mai kuɗin duniya ya yi tayin sayen kafanin Sadarwa na Twitter kacokan

 

Doge Father Elon Musk yayiwa GABAKI DAYAN SHARES din kamfanin TWITTER kudin GORO inda yace idan har an siyar mas duk guda Daya akan $54.20 dollar zai bayar da kudin gabaki daya IN CASH.

Kudin zai kama dalar Amurka BILIYAN $41. 


Elon Musk yanason TWITTER ta fifita Doge akan BITCOIN, sai dai a safiyar yau ne hukumomin TWITTER suka

TABBATAR da cewar bazasu shigar da Elon Cikin BOARD nasu ba saboda baram-baramar sa duk da cewar ya sayi. 

Wasu bayanai da ya miƙa wa hukumar kula da harkokin kuɗi ta Amurka sun nuna saƙonnin da Musk ya tura wa majalisar zaɓaɓɓu na Twitter cewa ya yanke shawara a ƙarshen mako cewa ya kamata kasuwancin kamfanin ya zama mai zaman kansa.

An gayyaci Mista Musk ya kasance cikin majalisar zaɓaɓɓun kamfanin amma Twitter ya sanar ranar Lahadi cewa ya janye tayin da ya yi masa.

Cikin bayanan, Musk ya ce ba ya son "je-ka-ka-dawo" sannan ya ce: "Tayi ne mai tsoka kuma masu hannun jarinku za su so shi."


Zai ɗauki matakin sayar da hannun jarinsa na Twitter idan har ba a karɓi tayin nasa ba, a cewarsa.


"Wannan ba barazana ba ce, kawai dai ba zai zama zuba jari kai waye ba idan ba a samu sauyin da ake buƙata ba," in ji shi.

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement