DAREN LAILATUL QADRI - DA KUMA FALALAR GOMAN KARSHE NA WATAN RAMADAN.
DARAJOJIN DAREN LAILATUL QADRI :
– A cikin shine Allah ya saukar da Alqur’ani Mai girma daga laihul mahfuz.
-Daren lailatul qadri shine dare daya wanda yafi watanni dubu.
-Dare ne mafi aminci domin cikin shi ne mala’iku karkashin jagorancin mala’ika Jibril Alaihis Salam ke zuwa cikin duniyar nan.
-Hakama Allah ya kira shi dare mai aminci, shi yasa tabi’in nan Mujahid yace shine dare mafi aminci a shekara baki daya.
-A cikin sa ake budget na shekara n abunda dan Adam zai samu.
–A cikin daren lailatul qadri ne Allah ke gafarta wa dukkan bayin shi masu ibadu.
ABUBUWAN DA AKE BUKATAR YI A DAREN LAILATUL QADRI
-Dagewa da ibadu.
-Kaskantar da kai da kuka ga ubangiji.
Ana bukatar yawaita fadar ‘ALLAHUMMA INNAKA AFUWAN TUHIBBU AFUWA FU ANNAH’
saboda kaunar shi garemu da rahamar shi yayi mana bayani game da kwana kin da ake neman ta akwai darare kamar haka 21-23-27-29
Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace mu nemi daren lailatul qadri a wadannan kwana kin
ALAMOMIN DAREN LAILATUL QADRI
idan daren yazo lokachin sanyi to za’a sasauta, Idan yazo ne lokachin zafi haka ma, Sannan da safe idan rana ta fito zaka ganta babu zafi.
Yan uwa musulmi masu albarka mu tashi tare da iyalan mu baki daya domin neman wannan rahamar ta ubangiji.
Idan kayi sallar tahajud babu laifi kayi tarawihi, yana da kyau kada ka kwanta kayi ta bacci.
DAGA BAKIN
Prof. Shiekh Umar Sani Fagge.
DAREN LAILATUL QADRI
Ayi sauraron Lafiya Kuma Ya Datar da mu A Duniya Da LAHIRA ya samu Cikin Yan tatun bayin Sa.
Alkhairin Goman Karshe Na Ramadan
Allah kayi salati da tasleemi ga Shugaban mu Annabi Muhammadu da iyalinsa da sahabban sa da dukkan mataimakan sa da masoyan shi har zuwa ranar sakamako.
Ya ubangiji ka amintar da jihar mu da kasar mu baki daya, Ya Allah Muna tawasuli da sunayen ka tsarkaka ka biya bukatun mu na alkhairi baki daya…
Ya ubangiji ka shiryi zuri’ar mu tare da mu baki daya.


0 Comments