4
Mutum 17 ne su ka sayi fom Din Takarar shugaban kasa jam’iyyar Adawa Ta PDP.
jam’iyyar Adawa Ta PDP ta gama sayar da fom din takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar, fom din wanda shine zai zama na share fagen zama marikin tutar jam’iyyar a zaben shekarar 2023.
Masu sha’awar tsayawa takara mutum 17 ne su ka sayi fom din. Inda jam’iyyar ta samu kudin da ya kai Naira miliyan 646 daga mutum 17 din da suka yankin fom din.
Jerin mutane da suka sayi fom sune kamar haka;
Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar.
tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto
Aminu Waziri Tambuwal da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya
Anyim Pius Anyim.
Sauran masu sha’awar takarar sune;
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad.
Gwamna Wike na jihar Ribas
Gwamnan Akwa Ibom Udom Emmanuel,
tsofaffin gwamnoni Peter Obi da Fayose sai wani mazaunin Amurka Nwachukwu Anakwenze da kuma Dele Momodu.
Mohammed Hayatu-Deen da Sam Ohuabunwa, da Cosmos Ndukwe, Charles Ugwu, da Chikwendu Kalu sai mace tilo wato Oliver Tareila Diana; su ma sun yanki tikitin.


0 Comments