Ad Code

Responsive Advertisement

WANI BABBAN DAN KASUWA YA MUSULUNTA A KANO MAI SUNA Mr. Joseph inda ya kuma Hamza.

Fitaccen Dan kasuwa mai sana'ar sayar da takalma a birnin Kano, kuma Dan jihar Delta, mai suna Mr. Joseph Johnson ya ce wani mafarki da ya taba yi, na daga cikin da lilin rugumar Addinin musulunci, baya ga sha'awar sa ta ya zamto musulmi.


Mr. Joseph Johnson ya bai yana hakan a harabar shalkwantan hukumar Hisbah da ke unguwar sharada, inda ya karbi Kalmar musulunci ta hannun, Babban kwamandan hukumar Hisbah.


Mr. Joseph Johnson Wanda bayan an rada masa Kalmar musulunci kuma nan ta ke ya ce, yana da sunan da ya fi so kuma ya ke burga shi shine sunan Hamza, furta hakan ke da wuya sai, Babban kwamandan hukumar Hisbah ya tambayi ko kana son sunan? Sai ya amsa eh ina so, sai Babban kwamanda ya ce daga yau sunan ka Hamza.


Mr. Joseph Johnson Wanda a yanzu ya zama Hamza a sakamakon shiga addinin musulunci, ya kara bayin cewar a kwana kin nan, ya na yawan yin mafakin ga shi a cikin dimbin yan uwa musulmi Su na yin sallah, Wanda hakan ya da da ba shi kwarin gwaiwar barin addinin kistaci izuwa na musulunci.


Ya na na ta cewar a tsawon shekaru goma da ya yi a jihar Kano, dukkan abokan kasuwancin sa musulmi ne, kuma dabi'un kasuwancin su, da al'adun su da addinin musulunci dukk ya na burge shi kuma ya ce, ya zabi karban kalmar shedar shiga addinin musulunci, ba ta hannun kowa ba sai ta hannun hukumar Hisbah, sabo da aiyukan Hisbah na yaki da badala, da karuwanci da shan kayan san yame da sauran su.


Ya ce aiyukan Hisbah a jihar Kano na da mutukar muhimmanci kuma hakan ya na burge shi ka na ya bukaci jama'a jihar Kano da su cigaba da bawa hukumar Hisbah dukkan goyon bayan da ta kamata.


Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina, da Babban mukadashi kwamanda mai kula da sashin aiyuka na musanman, malam Hussain Ahmad cidiyar kuda tare da sauran ma'aikatan sashin, Da'awa na daga cikin wadan da suka jagoranci, lakabawa , Mr. Joseph Johnson Wanda yanzu ya zama Hamza.

Written by 

Lawan Ibrahim Fagge

Public Relations Officer.

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement