Ana wata Ga wata budurwa ‘yar Najeriya, Fehintoluwa Okegbenle, ta yi tafiyar yawon buɗe ido a Najeriya, inda ta zagaye har zuwa jihohi 22 a bisa babur.
Da ta ke bayar da labarin ta a Twitter, budurwar ta bayyana cewa ta kammala tafiyar cikin sati ɗaya. A cikin kwanaki bakwai, ta zaga jihohi irin su Ogun, Edo, Enugu, Kaduna, Kano, Bauchi, da sauran su.
Budurwar ta bayyana ba ta fuskanci ƙalubalen tsaro ba yayin tafiyar ta
Fehintoluwa ta wallafa wasu hotuna a shafin sada zumuntar inda ta bayyana cewa taji daɗin tafiyar sosai.
Da take amsa tambayoyi kan yadda ta samu ta tsallake jihohin arewacin ƙasar nan da ake fama da rashin tsaro, ta bayyana cewa tayi saa bata fuskanci matsala ko ɗaya ba.
Ta ƙara da cewa tana la’akari sosai da dukkanin abinda ba ta gamsu dashi ba akan hanya. Kafin ta bi hanya, tana haɗa bayanai akan hanyar kwana guda kafin ta bi hanyar.
Nayi mamakin yadda na zagaye Najeriya akan babur dina, jihohi 22 a cikin kwana bakwai.
Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ekiti, Kogi, Abuja, Kaduna, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Benue, Cross River, Ebonyi, Enugu, Anambra, Delta, Edo, Ondo, Ogun, Lagos.
Naji dadi sosai, wannan yawon bude ido ne mai cike da abubuwan al’ajabi.Mutane sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari da faru.
Wallafar da tayi, ta janyo mutane da dama sun bayyana ra’ayoyin su. Ga ƙadan daga ciki:
@stgorzhye ya rubuta cewa
Ya ki kayi wajen wuce yankunan arewacin Najeriya masu fama da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga
@imitoriyin ya rubuta
Mace ce ke. Kina nufin ‘yan bindiga ba su kai miki hari akan hanya ba?
@lord_barns ya rubuta
Jihohi 22 cikin kwanaki bakwai? Duk girman arewa kin zagaye ta tare da wasu jihohin? Da ace babur ɗin ki na magana, da ya faɗi baƙar wahalar da yasha
@blessmich85 ya rubuta
Gaskiya ke ta daban ce. Na yaba wa jarumtar ki.
KARANTA..... YANDA ZAKA GANO SUNAN WANDA YA KIRA KA DA PRIVATE NUMBER A SAUKAKE.
KARANTA..... Library Da tafi kowacce Kyau A fadin Duniya.
KARANTA..... Cikaken bayani akan Fasahar Zamani Kashi Na Daya.

0 Comments