Tofa Matar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ta tashi kan ‘yan Najeriya da dama bayan ta bayyana cikin wasu kwankwas-kwankwasan kaya wadanda suka dau jikin ta kwarai, LIB ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa akwai maganganu da ake yi na cewa ana kokarin jawo tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dawo ya mulki Najeriya a shekarar 2023, idan har hakan ta tabbata, daya daga cikin gwamnoni masu ci zai iya fitowa a matsayin mataimakin sa.
Akalla daya daga cikin gwamnonin nan guda biyar da suka fito daga Arewa, ana kyautata zaton za su goyawa tsohon shugaban kasar baya a matsayin mataimaki a zaben na shekarar 2023.
Ga jerin gwamnonin a kasa:
1. Gwamna Nasir El-Rufai
2. Gwamna Yahaya Bello
Kamar yadda masu sharhi kan al’amuran siyasa suka bayyana shi a matsayin daya daga cikin masu kare shugaban kasa, gwamnan na jihar Kogi ya yi suna sosai musamman a wajen matasa da suke kira gare shi da ya fito takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
3. Gwamna Babagana Zulum
Kokarin da gwamna Zulum ya yi wajen kawo karshen matsalar ‘yan Boko Haram da suke jihar Borno ya sanya ya zama daya daga cikin shugabanni da bai kamata su fito su yi yakin neman zabe ba idan har ya bukaci fitowa takarar shugaban kasa.

0 Comments