IYAYE MATA MASU GIGIWA KU BI DUNIYA A HANKALI.
'Yar uwa Musulma kar ki bari Tiktok da Instagram ya rudeki har ki fara tikar rawa kina girgiza duwawu ki saka a Tiktok da sauran kafofin sada zumunta ana miki ruwan likes da comments ki dauka burgewa ne, hakanan kar ki yadda sana'ar film da wakokin zamani ya rudeki.
Ya kamata Celine Dion ta zama darasi a gareku mata, Celine Dion 'Yar Kasar Canada ce, shahararriyar mawakiya ce da ta sanu a duk duniya, duk inda mace ke kaiwa a tashe ta kai a duniya imma bata wuce ba, yanzu tana da shekaru 56, amma ku dubi yadda ta dawo.
Duniya ta sallameta, ko labarinta ma ba'ayi, komai nata ya canza, shi kansa kyawun jiki da kyawun fata da dirin jiki da tsayayyen nono da take takama dashi a wancan lokaci yau an wayi gari duk sun gushe sun gujeta
Har abada ba zata sake komawa yadda take ba, a yanzu ko tayi tsirara babu namijin da zai ji sha'awarta balle ya nemeta da soyayya ya kashe mata kudi.
To haka duniya take sallamar mutumin da ya auri duniya, kar ki/ yadda 'yan duniya su rudeki ki tsaya shririta da bata lokaci wai ke 'yar gwagwarmayar ko celebrity, ki rufawa kanki asiri kiyi aure.
Akwai nassin Qur'ani inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa:
"Duk wanda muka bashi tsawon kwana a duniya to sai mun nakasa halittarsa, shin ba zaku hankalta ba?" -Qur'an.
Masu karin magana sunce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
To jama’a Ba iya Mata Harmu muma maza Muguji Miyagun dabi'u Da mugayan Halaye wanda Zasu Kai mu Su baru.
Allah ka datar da mu Duniya Da Lahira.
Allah Ka sa mu hankalta.
Whitten by Datti Assalafi.
Post by msz

0 Comments