Salam ma'abota wannan Shafin namu namu mai albarka. Darasin mu na Yau shine ∆ROOTING∆ kamar yadda taken darasin ya nuna.
Mutane da dama suna ta tambayana akan yadda ake yin rooting, duk da dai munyi bayani akansa watannin baya Amma a sakamakon ba muyi cikakken bayani akansa ba a wancen lokaci shiyasa Yanzu na sabuntashi tare da yin cikakken bayani a kai.
Rooting ba sabon Abu bane. Amma haryanxu wasu basu san abun da yake nufi ba.
Shi yasa Yau mukayi Dan takaitaccen bayani akansa. Batare da na cikaku da surutu ba ga abin da yake nufi
®ME AKE NUFI DA ROOTING:- a takaice dai rooting hanyace da ake canja waya daga tsarinta na company ma' ana idan Kayi rooting din wayarka to xaka samu damar canza saitin da taxo dashi daga company ta hanyar samun cikakken iko amfani da wayarka.
AMFANIN ROOTING
Rooting yana da amfani da dama kamar haka...
1) ldan Kayi rooting din wayarka zaka samu damar share duk wani application da wayar tazo dashi akanta idan Baka so shi.
2) Haka kuma zaka samu damar moving din duk wani application da Kayi installed din zuwa memory card din ka domin wayar ta samu cikakken gurin aiwatar da ayyukanta.
3) Akwai wasu application masu matukar muhimmanci Wanda idan Baka yi rooting din wayarka ba zaka ka samu damar aiki da su ba ko kuma Baza ka samu cikakkiyar damar amfani da su ba kamar su #lucky patcher, #Es file explorer, game booster dama sauransu.
4) Rooting yana kara karfin battery da kuma dadewar caji sosai.
Anan zamu diga Aya sai A kasan ce damu A wani sabon darasin Mai zuwa inda zamu dura daga inda muka tsaya.
Zamu tashi
# ILLOLIN YIN ROOTING #YADDA AKE YIN ROOTING DA COMPUTER.

0 Comments