Ad Code

Responsive Advertisement

SABON GIDAN TALABIJIN NA QAUSAIN TV YA NADA UMAR M Shareef.

Umar SHAREEF A MATSAYIN JAKADA

Sabon Gidan Talabijin na Qausain ya nada Shahararren Mawaki Umar M. Shareef a matsayin jakadansa na farko a Kaduna.


Babban Shugaban Kamfanin Na Qausain Group, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a yayin kaddamarwar wanda gidan Talabijin din ya shirya a harabar ofishinsa dake Sultan Road GRA Kaduna a wannan makon.


Shugaban Kamfanin ya bayyana jin dadinsa tare da kuma mika godiyarsa ga Allah SWT da kuma ilahirin ma'aikata da wadanda suka bada gudumuwa har wannan gidan talabijin ta tabbata.


Malam Nasir ya bada tabbacin cewa gidan Talabijin din zai ta fi daidai da zamani kamar sauran manyan Gidajen Talabijin na Duniya, tare da kare dukkan wani hakkin da ya rataya a wuyansu na ganin sun samar da ingantattun bayanai da nagartaccen ilmantarwa domin amfanin al'umma bakidaya.. 


Shi ma a nasa jawabin Babban Daraktan Qausain, Alhaji Musa H. Isa, ya bayyana cewa sun samar da tashar Qausain TV ne daidai da zamani da kuma bin duk wasu ka'idoji na samar da ingantaccen gidan Talabijin.

Musa H Isa, ya kuma gabatar da fitattacen Mawaki Umar M Shareef a matsayin jakadan tashar ta Qausain TV.

Inda shi ma mawakin ya bayyana jin dadinsa tare da alkawarin kawo cigaba mai dorewa a matsayinsa na jakadan tashar.


Tun da farko a tsokacinsa, Babban Manajan tashar, Umar Faruk Adam ya nemi goyon baya daga al'umma da ganin sun mara wa gidan Talabijin din baya ta fuskar karfafa togwiwa da kuma kawo tallace-tallace.


Ya kuma kara da cewa sun samar da hanya mai sauki ga masu sha'awar sanya hannun jari ko son kulla alakar kasuwanci da Gidan Talabijin din na Qausain TV.


www.qausaintv.com , info@qausaintv.com

Facebook: @qausaintv, YouTube: @qausaintv, Instagram: @qausaintv

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement