Ad Code

Responsive Advertisement

Dalilin da yasa Facebook, WhatsApp da Instagram Suka tsaya Na Tsawan Awa Uku A jiya.

 

Shugaban Mai Dandalin Sada Zumunta ta Facebook. Ya aike, da sakon Neman afuwar masu amfani da su inda ya kara da cewa yana kokarin shawo kan matsalar.



Rahotanni daga sassan na duniya na cewa manyan shafukan sada zumunta na Facebook, WhatsApp da Instagram ba sa aiki yayin da miliyoyin mutane a sassan duniya ke kokari su yi amfani da su.


A yankin Amurka lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin da misalin karfe 11:45 inda manyan shafukan suka daina aiki kwata-kwata.


A Najeriya, wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir da ke Kano a arewacin kasar, ta tabbatar da cewa shafukan sun daina aiki a lokacin da muka tuntube ta.


Kazalika wakilanmu da ke Abuja sun ce wadannan dandali na sada zumunta duka ba sa aiki.

A shafinsa na Twitter, kamfanin na Facebook ya ce ya samu labarin wannan lamari, kuma yana iya bakin kokarinsa “wajen ganin ya shawo kansa ba tare da bata lokaci ba, muna neman gafara kan wannan lamari.”


Akalla mutum biliyan 2.85 ke amfani da shafin Facebook a duk wata a cewar kamfanin kididdiga na Statista.

Shi kuwa WhatsApp an yi kiyasin yana da mutum biliyan 2 da suke amfani da shi a duk wata yayin da Instagram ke da mutum sama da biliyan daya.


Kamfanin bai fadi dalilin da ya haifar da wannan katsewa ba, duk da cewa ya ce yana kokarin shawo kan matsalar.


Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement