Kulafadin Ƙungiyar PSG tana cigaba da tattaunawa da Sergio Ramos domin ta siye shi bayan kwantiraginsa ya ƙare da ƙungiyar Real Madrid a kakar bana
Manchester United tana ƙoƙarin ganin siyo ɗan wasan gaba na Everton ɗan ƙasar Ingila Dominic Calvert-Lewin ɗan shekaru 24
Ƙungiyar Everton tana fatan ta kashe Arsenal a siyan ɗan bayan ƙungiyar Brighton dan shekaru 23,Ben White wanda Gunners ta yiwa ɗan wasan tayi har sau biyu yana ƙin amsa
Barcelona tana fatan siyar da ɗan wasan bayan Sifaniya Junior Firpo ga ƙungiyar Leeds United a kwanaki masu zuwa sannan ta shirya bayar da aron Miralem Pjanic ga kungiyar Juventus ko Tottenham
Liverpool tana fatan siyan ɗan wasa Brighton ɗan shekara 24 ɗan kasar Mali, Yves Bissouma da ɗan wasan Ajax ɗan ƙasar Netherlands Ryan Gravenberch ɗan shekaru 19 domin maye gurbin Georginio Wijnaldum daya koma PSG a cikin wannan kakar wasannin
Tottenham ta bi sahun Everton wajan ganin ta siyi ɗan wasan bayan ƙasar Ingila mai shekaru 28 Conor Coady daga Wolves
Daga Msz


0 Comments