Bikin bayar da sandar da aka yi a filin wasa na Sani Abacha a Kano a ranar Asabar ya samu halartar sarakuna na ciki da wajen Najeriya.
Gwamnan Kano Umar abdullahi Ganduje ya gabatar da sandar gima ga Sarkin Kano Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero bayan shekara ɗaya kan gadon sarautar Kano.
Mai martaba Sarkin kano Alh Aminu Ado Bayaro ya karbi shahadar zama sarkin kano na 15 ajerin sarakunan fulani.
Mai girma Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shine ya bashi sandar Mulki sannan ya karbi rantsuwa daga wajen limamin kano.
Mataimakin shugaban kasa Prof Yemi osibanjo shugaban majalisar Dattijai Sen. Ahamad lawan, shugaban Ma'akatan fadar gwamnatin Tarayya Prof. Ibrahim Gambari ,SFG Boss Mustapha Ministoci, da Gwamnonin jihohi 8 da Gwamnan damagaran , jakadun kasashe da sarakonan gargajiya a ciki da wajen kasar nan sama da 110 ne suka samu halatar wannan gagarumin bikin bada sandar.
Uba a garin mai martaba sarki Alh Aminu Dantata shima ya sami halatar wannan. taro kuma ya saka Albarka sannan. yayi fadakarwa ga shugabanni .
Yadda aka sanyawa mai martaba sarki malafar dabo.






0 Comments