Ad Code

Responsive Advertisement

Ɗangote Ya Fi Wasu Ƴan Siyasar Fahimtar Matsalolin Ƴan Najeriya- In Ji Gwamnan jihar Bauchi.

 


Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce shugaban rukunin kamfanin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya fi wasu ƴan siyasar fahimtar matsalolin ƴan Najeriya

Gwamna Bala ya yi wannan bayanin ne a loƙacin da gidauniyar ɗangote su ka kai masa ziyara ta musamman.

A cewarsa, ɗan kasuwar ya taimakawa wajan tallafawa mata da wasu ƴan Najeriyar

“Ɗangote bai tsaya kawai ba wajan gina makarantu da bada tallafi a fannin kiwon lafiya a duk faɗin duniya, ya cigaba wajan kafa rukunin kasuwanci, wanda hakan yasa wasu ƴan Najeriyar suka samu maciya abinci, saboda wannan hangen nesan na sa, ya nuna cewa ya fi wasu ƴan siyasar fahimtar matsalolin Najeriya tunda yana taimakon jama’a akan yadda za su lura da iyalensu” in ji gwamna Bala Mohammed

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement