Wata sanar da ma'aikatar yada labarai da al'adu ta fitar, ta ce Minista Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar a Abuja a ranar Juma'a.
Sanarwar ta ce Minista Mohammed ya ce ana amfani da shafin wajen raba kawunan ƴan ƙasar.
Lai Mohammed ya kuma ce ya bai wa hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasar NBC ta fara shirye-shiryen ba da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na intanet.
Sai dai gwamnatin NAjeriyar ba ta fayyace abin da take nufi da wannan mataki ba ya zuwa yanzu.
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da shafin Tuwita ya goge wani saƙo cikin jerin saƙwannin da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa yana gargaɗin ƴan awaren IPOB
Tun bayan cire saƙon shugaban ƙasar fadar Shugaba Buhari ta ce tana sane da matakin da Twitter ya ɗauka, kuma ta aika da buƙatar neman jin dalilin da ya sa kamfanin ya goge saƙon.
Tuni dai kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce za ta kalubalanci matakin gwamnatin a kotu, a wani sako da ta wallafa a Tuwita din.
.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Jim kaɗan da fitar da wannan sanarwa sai ƴan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta musamman Tuwitar.
Tuni aka ƙaddamar da maudu'ai har huɗu a shafin na Tuwita don tattaunawa kan batun, da suka haɗa da #So Twitter da aka yi amfani da shi kusan sau miliyan ɗaya a ƙasa da ɗaya da #Twitter in Nigeria 100,000, da #Using Twitter da aka yi amfani da shi sau 239,000.
Sannan akwai maudu'in #Federal Government mai 36,000 da kuma #TwitterBan mai saƙonni 1,384. AKwia kuma irin su #Jack da #Lai Mohammed da #Twitter in Nigeria da #Suspending Twitter da dai sauran su.
Ƴan ƙasar da dama ne suka dinga bayyana ra'ayoyi daban-daban kamar haka:
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a 2019 Alhaji Atiku ya wallafa cewa: "Ina fatan kar wannan ya zama saƙona naƙarshe a Tuwita."



0 Comments