Maniyyata A Kano Sun Bayyana Alhini Game Da Janye Aikin Hajjin Bana.
Mahmud Ibrahim Kwari
Da
Hadiza Kyari
Dubi ra’ayoyi
Maniyyata aikin hajin bana da masu kamfanonin jigilar alhazai ta jirgin yawo a Najeriya na bayyana alhini dangane da sanarwar hukumomin Saudiyya na janye aikin hajji ga ‘yan kasashen waje.
A Ranar asabar mahukuntan kasa mai tsarki suka fitar da sanarwar cewa, ‘yayan kasar saudiyya da baki mazauna can ne kawai ke da damar gudanar da aikin hajjin bana, amma su ma bisa cika sharrudan kiyaye kamuwa ko yada cutar Corona da aka shimfida.
Kamar sauran kasashe, yanzu haka dai wannan mataki ya dagula lissafin maniyyata daga Najeriya
Wasu daga cikin dinbin masu aniyar sauke farali a bana daga jihar Kano da Muryar Amurka ta yi hira da su sun nuna bacin ransu game da wannan lamarin saboda sun sa a ran su cewa sun riga sun zama alhazai.
Su ma masu kamfanonin dake shirya jigilar alhazai zuwa kasa mai tsarki ta jirgin yawo sun koma game da wannan yanayi da aka tsinci kai.
Fiye da alhazai dubu 90 ke sauke farali a kowace shekara daga Najeriya kuma kimanin dubu 7 daga cikin su ‘yan jihar Kano ne.
By VoA. Hausa.


0 Comments