A ranar Alhamis ne Malam Sabi'u ya fara shaida wa manema labarai wannan mataki nasa da wadda makarantar New Oxford Science Academy da ke unguwar Chiranchi ta ɗauka.
Ya ƙara da cewa hukumar makarantar ba ta ɗauki matakin ba sai da ta tuntuɓi iyayen yara don jin ta bakinsu.
A haƙiƙanin gaskiya mun fito da wannan tsari ne ganin yadda duniya ke ta tururuwa wajen amfani da kuɗin intanet," a cewarsa."Kuma Alhamdulillah yanzu idan kuka duba ƙasashe irin su El-Salvador sun halatta cryptocurrency ya zama kuɗin kashewa a ƙasar.
Ya kara da ce ya ga kamatar ya shiga cikin tsarin tun a farko-farkonsa kafin lokaci ya ƙure, ya zama damar ba ta da yawa.
By msz.


0 Comments