Ad Code

Responsive Advertisement

Halin da ake ciki a Najeriya na neman wuce gona da iri, a cewar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo


Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki .


by  Aisha Musa 


 Halin da ake ciki a Najeriya na neman wuce gona da iri, a cewar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.


A wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan, Obasanjo ya ce an kadarci dora kasar da zama babbar kasa amma mummunan shugabanci ya zama babban cikas a gare ta .


A halin yanzu, tsohon shugaban kasar ya ce akwai bukatar sauya halin da Najeriya ke ciki Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya magantu a kan halin da kasar ke ciki kuma ya yanke shawarar cewa Najeriya ba ta a inda Allah ya kadarceta da kaiwa a cikin tsarin kasashe.


 Ya koka kan cewa maimakon ta zama ƙasa mai yalwar madara da zuma, abin takaici ta zama "ƙasar da ke kwararar da ɗaci da baƙin ciki", yana mai roƙon ‘yan Najeriya da su sauya labarin, jaridar Punch ta rahoto. 


Tsohon Shugaban kasar ya yi magana ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a Cibiyar Matasa ta dakin karatun shugaba Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, yayin gabatar da wani littafi Mai taken: ‘The Man General President Olusegun Obasanjo, GCFR’.

 An rubuta shi ne don girmama Obasanjo da kuma bikin murnar cikarsa shekaru 84 da haihuwa, jaridar The Nation ta ruwaito. Read more:.


by msz.


Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement