Gabatarwa by
by
isah mukutar
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da nadin Abdurrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC jiya Laraba, bayan zaman sa’oi biyu ta na nazarin bukatar da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar na neman a gaggauta amincewa da nadin shi.
Da yake jagorantar zaman, shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan ya yi kira ga majalisa ta duba bukatar da shugaban kasar ya gabatar na neman a amince da zaben Abdurrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar, bisa tsarin dokar aikin hukumar na 2003 sashe na 2 sakin layi na 3.
Bayan shugaba Buhari ya gabatar da sunan Abdurrasheed Bawa ga majalisa domin rike wannan mukamin, wadansu suka fara korafin cewa, bai kamata a bashi wannan mukamin ba bisa zargin cewa, shi kansa hukumar EFCC ta taba gayyatarsa domin yin bayani a kan sayar da manyan motoci 240 da hukumar ta kwace ga mukarrabansa, zargin da hukumar EFCC ta karyata.
Abdurrasheed Bawa, wanda ya fara aiki da hukumar EFCC a shekara ta 2005, shi ne shugaban hukumar EFCC na 5. Ya gaji Ibrahim Magu wanda har zuwa lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shi a watan Yuli 2020, ya ke matsayin riko domin kasa samun amincewar majalisa


0 Comments