DABARUN RUBUTUN WAKA
KASHI NA BAKWAI
Daga
Nasir G Ahmad
RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA
Barkan mu da sake kasancewa a cikin wannan topic inda zamu dura da bayani a cikin sa.
A makon jiya muka karashe magana kan ma'auni ko karin waka. To yau kuma za mu duba:
2. DANGO
Dango na nufin sadara ko layi guda na rubutacciyar waka. Wato yankin zance wanda akan harhada ya tayar da waka. Sau da yawa dango kan ci gashin kansa, wato ya ba da cikakkiyar ma'ana, ba tare da jinginuwa da wanda ya gabace shi ko wanda ke biye da shi ba. Misali:
jama'a ku taho zan wallafa,
zan wakar sangartacciya.
(Baba Maigyada Agege)
3. BAITI
Dangogi su ne ke harduwa su ba da baitin rubutacciyar waka. Baiti kan zo a tsarin gunduwoyi (layuka), wadanda ake kira dangogi, kamar yadda bayani kan dango ya gabata.
Mu kwana nan.
anan zamu diga aya sai muhadu a Kashi na gaba.
Daga
Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al'ummar hausawa.
Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za'a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu,
ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.


0 Comments