FASALI NA BIYU
{ ALWALA }.
Alwala wajibi ce a kan duk mai sallah , kuma haske ce,yin alwala shirye-shirye ne da bawa zai sadu da (Ubangijinsa,)yana mai tsarki .
Alwala tana tsarkake gabban mutum daga zunubai A cikin ta akwai abubuwn da ake kira {farillan alwala}da (sunnoni)da(Mustahabbai)da abubuwan da suke warware ta .
{FARILLAN ALWALA}
Farillan alwala guda bakwai ne :-
1- Niyya
2- Wanke fuska baki daya.
3- Wanke hannuwa izuwa guiwarsu
4- Shafar kai
5- Wanke ƙafafuwa izuwa idan sawu.
6- Cuccudawa
7- Gaggautawa .
{ SUNNONIN ALWALA }
Sunnunin alwala guda takwas ne :-
1- Wanke hannaye izuwa wuyansa
2- Kuskurar baki
3- Shaka ruwa
4- Face ruwan
5- Juyo da shafar kai
6- Shafar fatun kunnuwa
7- Sabunta ga dukan gaɓɓai
8- Jerantawa tsakanin farillai.
{MUSTAHABBAN ALWALA}
Mustahabban alwala guda goma sha daya ne:-
1- Yin bisimilla Yayin farawa alwala
2- Goga asuwaki
3- maimaita wanwankewa
4- Farawa daga goshi
5- Jeranta sunnoni
6- Karancin ruwa a bisa gaɓɓai
7- Farawa da wanke gaɓɓin dm san hg
8- Waje tsarkake
9- Tsetsefe gemanya sadauka
10- Tsetsefe yatsun ƙafafuwa
11- Ajiye ƙwarya daga dama in ta kasance mai buɗɗen baki cikin.
{FADAKARWA!}.
Ana so mai yin alwala ya kiyaye, idan abin da ya zuba ruwa alwala ya kasance buɗaɗɗe ne kamar, ƙwarya, gwangwani, roba da makamantansu.
Sai ya ajiye daga gefan hannun dama, idan kuma abin da aka zuba rawan alwalar mai rufaffen baki ne, kamar buta, sai ya ajiye ta daga gefan hannun hagu.
[ABUBUWAN DA SUKE WARWARE ALWALA]
Masu warware alwala sun kasu kaso biyu:-
1. Karrai
{2. Sababai}
sababai sune:-
1- Barci mai nauyi
2- Maye
3- Suma
4- Bugun aljan
5- sumba ko kiss
6- Shafar mace ko namiji da nufin jin dadi
7- Shafar azzakari da cikin tafin hannu ko yan yatsu.
8- Ridda
9- Kokwanto.
Daga nako
musa S ZAGE


0 Comments