Ad Code

Responsive Advertisement

[Layya da abin da ta kunsa a takaice ce].

Daga. DMuhammad Kabir Asgar*

Mecece layya?

Layya wajibi ce ga duk wanda ke da hali. Dabba guda daya ta wadatar ga mai gida da iyalinsa, in an sami kari to ya yi kyau. Ko da kuwa zai kai ga kowane mutum guda a ba shi dabbarsa.

  Lokacin yanka dabbar layya yana farawa ne daga sa’add limamin idi ya yanka dabbarsa a ranar sallar har zuwa faduwar ranar 13 ga watan Zhul Hijja.

Zubar da jinin shine abin da sharia ta ke so, don haka ba daidai ba ne a yi sadaka da kudin dabbar a maimakon yankawa.
Malamai sun ba da fatwa akan halascin yanka dabba bayan wucewar lokacin (ga wanda ke da uzuri karbabbe kamar wanda dabbarsa ta bata sai ya ganta bayan lokacin).

   *SHARUDDAN DABBAR LAYYA*   

1- Dole dabba ta zama daga cikin dabbobin ni’ima (Raquma, Shanu, Tumaki da Awaki).

2- Dole ne ta zama ta kai shekarar da sharia ta gindaya (Raqumi shekara 5, Shanu shekara 2, Tumaki da awaki shekara 1).

3- Dole ne dabbar ta zama ta kubuta daga aibi ko naqasa mabayyaniya (kamar makanta, karyewa, gurguntaka, rama mai tsanani, rashin lafiya da sauransu).

4- Dole ya zama mutumin da zai yanka dabbar ya mallake ta ne ta hanya karbabbiya a sharia (ba a yin layya da dabbar sata, ko ta kwace, ko ta aro, ko ta jingina ko wadda ake da tarayya a kan mallakarta).
An so mutum ya yanka dabbar sa da kansa in zai iya
Addu’ar da ake yi wajen yanka ita ce: ( ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻨﺎ )
Ana son a sami wuqa mai kaifi don gujewa wahalar da dabba.

WACE DABBA TA FI?

Akwai fifiko na JINSI
Akwai kuma na SIFFA
Dangane da jinsi an fi son
- Raqumi
- Sannan shanu
- Sannan Tumaki
- Sannan Awaki
- Sannan tarayya akan Raqumi (mutum bakwai)
- Sannan tarayya akan Saniya (mutum bakwai)
Dangane da siffa ana son
- Mai kiba
- Mai tsadar farashi
- Mai kyaun siffa
- Mai koshin nama
- Da dai sauran siffofi na kamala
   
    YA AKE RABAN NAMAN LAYYA?

- Babu laifi a ci a gida
- Sannan a yi kyauta
- Da sadar da zumunci
- Da sadaka
- Sannan a taskace
- An so a fifita bai wa mabukata (talakawa, marayu, zawarawa, baqi da sauran masu qaramin samu).

Ba mustahabbi ba ne mutum ya yi aski bayan ya yanka layyarsa.
 Idan mutum ya sai dabba da niyyar layya bai halasta yai sai da ta ko da da nufin canzawa ne ba sai dai in zai sayar ne ga wani wanda shima layyar zai yi ko kuma ya kyautar
Matafiyi na yin layya kamar yadda mazaunin gida ke yi
Wakilin maraya yana da damar ya yi masa layya a cikin dukiyarsa bisa ma’arufi.
 Ya halasta mutum ya ci bashin kudin da zai sayi dabba ko ya ci bashin dabbar layya.

 Hakanan kuma ya halasta ga wanda ake bin sa bashi ya jinkirta biyan bashin don ya sai dabbar layya
Idan aka bai wa mutum kyautar dabbar layya yana da cikakken tasaruffi a kan dabbar don ta zama dukiyarsa
Layya na cikin ciyarwa, don haka mace na iya yin layya da dukiyar mijinta ga iyalansa ko ba da izini ko saninsa ba
Idan layya ta hadu da aqiqar radin sunan jariri kuma guda daya ake da halin yi.

 Tana gabatar da wacce ta fara zuwa ne in ba rana daya suka zo ba. In kuwa rana daya suka zo to sai a yi aqiqa
Ana yi wa mamace layya idan yai wasiyyar a yi masa layya a cikin daya bisa ukun dukiya.

KAR A MANTA DA YAWAN KABARBARI A CIKIN KWANAKIN SALLAH

Allah ya sa mu dace

Daga naku
 musa S Zage

karkuman ta da share zuwa ga ƴan uwa da abokan arziki.

Domin samun wasu shirye shiryen mu
Hausa

Domin kalan ranar ARFAT sai a biyu a website din mu.ranar.


Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement