Ad Code

Responsive Advertisement

[KOKASAN AMFANIN KANKANA GA JIKIN DAN ADAM].



 DAGA NAKU
MUSA S ZAGE
       
  Kankana uwar ruwa ta nada amfani susai a jikin dan Adam musan man ma a lokacin da ta nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunannar ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke matukar taimaka ma idanu.
  Kankana tana da matukar mahimmacin kuma sananniya ce a cikin ‘ya’yan itatuwa, wadda ‘ya’yanta ke dauke da sinadarai masu gina jikin dan adam, kamar su vitamin B, niacin, folate da kuma irinsu magnesium, potassium, manganese, iron, zinc, phosphorus da copper.  async src="https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js">


    [WASU DAGA CIKIN AMFANIN KANKANA GA JIKIN DAN ADAM]

> Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen maganin cututtuka da dama.

> Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.

> Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan nitric oxide dake kara ma namiji karfin gaba.

> Tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma ciwon koda.

> Ya’yan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jiki lafiyar jinin dan adam.

> Tana da sinadarai masu kara karfin kashi  bone  da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban jiki {joints}.

> Zakin cikinta kuma na ba mutum karfi, tana kuma kara ma jiki ruwa.

> ‘Ya’yan kankana ana amfani dasu wurin magance ciwon diabetes, idan aka tafasa ruwa ‘ya’yan kankana 1litre na tsawon mintina 45, sai a ringa shan ruwan kamar shayi.

> Ya’yan kankana suna taimakawa wurin samun karfin jiki bayan rashin lafiya sannan kuma suna kara kaifin tinani.

.> ‘Ya’yan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji.

> Tana haifar da samuwar wadataccen barci.

> kankana na taimaka ma fata saboda sinadarin lycopene dinta.

      ALLAH YAKAREMU DA LAFIYA AMEEN.

               DAN NEMAN KARIN BAYANI SAI KU       
                    Email: musasszage@gmail.com
                      WhatsApp: +2348135986732
                         Facebook:  musa s zage
                           Twitter: musa s zage


Post a Comment

0 Comments

Ad Code

Responsive Advertisement