A baya bayannan Masana sun gano ta hanyar wata na'ura mai suna FRMI cewa bangaren kwakwalwa na gaban goshin Dan Adam shike taka rawa a yayin da mutum zai karya domin wajen Yana Kara nishadi kuma yayin da mutum zai kirkiro karya wajen Yana Kara takuruwa gwargwadon yawan karyar da mutum zai yi.
Wannan ya faru sanadiyar bincike Akan Masu laifi Yadda suke wahalar da Masu binciken Masu laifi ta yadda idan an tambayesu gaskiyar Abu sai Suyi karya Shi yasa wash Masana a shekarar 2003 suka kirkiro wata na'ura Mai suna (telegraph) wacce za'a daurawa Mai laifi a Kansa sai adinga gainin Hoton kwakwalwarsa ta screen din computer a yayin da zai karya sai a ga bangaren kwakwalwarsa na gaban goshi Yana nishadantuwa kuma Yana takuruwa Amman idan gaskiya zai fada sai aga wajen simul ba wata . Kuma binciken Masana ya Kara tabbatar dacewa wannan kwakwalwa ta gaban goshi itace take taka rawa idan mutum zai aikata wani laifi ko magudi kuma Nanne cibiyar fahimta da riskar Abu . Shi yasa idan Mutum ya Sami Matsala a wannan wuri sai ya koma kamar karamin Yaro.
Ya Kai Dan Uwa ko kasan alkur'ani ya fadi wannan tun a karni goma sha hudu da suka wuce inda Allah subhanahu wa ta'ala ya siffata makwarkwadar Abu Jahl da makwarkwada Mai karya Mai laifi. Domin kwakwalwar Abu Jahl ta gaban goshi da ita Yake karyata Annabi kuma da ita Yake shirya duk wani laifi da makirci. Allah subhanahu wa ta'ala Yana Fada:
( ﻛﻼ ﻟﺌﻦ ﻟﻢ ﻳﻨﺘﻪ ﻟﻨﺴﻔﻌﻦ ﺑﺎﻟﻨﺎﺻﻴﺔ)
( ﻧﺎﺻﻴﺔ ﻛﺎﺫﺑﺔ ﺧﺎﻃﺌﺔ)
Allahu Akbar ! Don haka Za muga cewa Lille Alkur'ani littafine Mai dacewa da kowne irin lokaci da kuma zamani.
daga naku
musa s zage
Domin Neman Karin Bayani Zaka Iya Tuntubarmu Ta Wayannan Hanyoyi Kamar Haka
Email: musasszage@gmail.com
WhatsApp: +2348135986732
Facebook: musa s zage
Twitter: musa s zage


0 Comments