Alkur'ani ya bayyana cewa hankaka ya koyar da Dan Adam yadda zai binne gawa acikin kissar yayan Annabi Adamu Guda biyu wato Habilu da Kabilu inda Allah (SWA) Yake cewa
( ﻓَﺒَﻌَﺚَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻏُﺮَﺍﺑًﺎ ﻳَﺒْﺤَﺚُ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻟِﻴُﺮِﻳَﻪُ ﻛَﻴْﻒَ ﻳُﻮَﺍﺭِﻱ ﺳَﻮْﺃَﺓَ ﺃَﺧِﻴﻪِ ﻗَﺎﻝَ ﻳَﺎ ﻭَﻳْﻠَﺘَﺎ ﺃَﻋَﺠَﺰْﺕُ ﺃَﻥْ ﺃَﻛُﻮﻥَ ﻣِﺜْﻞَ ﻫَﺬَﺍ ﺍﻟْﻐُﺮَﺍﺏِ ﻓَﺄُﻭَﺍﺭِﻱَ ﺳَﻮْﺃَﺓَ ﺃَﺧِﻲ ﻓَﺄَﺻْﺒَﺢَ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺩِﻣِﻴﻦَ ) سورة [ ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ] :
A yau Masana sun bayyana cewa hankaka shine tsuntsun da yafi kowane tsuntsu fasaha. A wani bincike da aka gudanar a Oxford dake ingila an jarraba fasahar hankaka ta yadda aka sa Nama a cikin wani kofi aka rufe da murfi zai aka ga hankakan Yana kokarin sa wani Kara domin ya cire murfi ya dauki naman dake cikin kofin Wanda wannan Yana nuna fasahar wannan tsuntsu.
Lalai alkur'ani yayi gaskiya da ya bayyana cewa hankaka Yana da hikima Harma ya koyar da Dan Adam yadda ake binne gawa.
masana-sun-gano-cewa-kwakwalwar-gaban ita ce take taka rawa wajen aikata wani laifi. Allahu Akbar ! Don haka Za muga cewa Lalai Alkur'ani littafine Mai dacewa da kowne irin zamani da kuma lokaci.
DAGA NAKU
MSZ
Domin Neman Karin Bayani Zaka Iya Tuntubarmu Ta Wayannan Hanyoyi Kamar Haka
Email: musasszage@gmail.com
WhatsApp: +2348135986732
Facebook: musa s zage
Twitter: musa s zage.
1 Comments
Nice post
ReplyDelete