بسم الله الرحمن الرحيم
(8) MENENE HADISI MUTASSILI?
Hadisi mutassili. shine hadisin da jinginansa ya sadu da jin kowane daya daga masu ruwayarsa. tun da farko har karshen sa. Ya tuke ga Annabi kokbai tuke ba. sai ga sahabi. shine dai. suna da banban ci da musnadi. bamban cin kuwa shine. dukkan musnadi mutasili ne. amma ba dukkan mutassili bane musnadi.
(8) MENENE HUKUNCINSA ?
Hukunci sa daya ne rukunan wanda ya gabata.
وما بسع كل راو يتصل
إسناده للمصطفى فالمتصل
(9) MENENE HADISI MUSALSALI?
Hadisi musalsali shine hadisin da aka rawaito shi daya bayan daya. a kuma hali daya. a suffa daya.
(9 ) MENENE HUKUNCINSA?
Hadisi musalsli da kyar yake kau cewa ya fita daga gidan Rairfi. amma fa asalin tantagayar hadisin. wato mataninsa.
مسلسل قل ما عل وصف اتى
مثل ا ما و الله انباني الفتى
کذاك فد حد ثنيه قاء ما
. أو بعد أن حدثنى تبسما
(10) MEMENE HADISI AZIZI?
Hadisi azizi shine hadisin da mutum biyu suka yi dai dai a cikin ruwayar sa, ko da bayan wadannan mutum biyu masu rawaya ko da yawa sun rawaito shi.
(10) MENENE HUKUNCINSA ?
HUKUNCINSA KO DAI SAHIHI KO HASANI KO RA'IFI.
عز يز مروي إثنين او ثلاثه
وبالله التوفيق.
sai a taremu a kashi na biyar.
daga dalibin ku
musa s zage.

0 Comments